Khan zai iya dambe da Mayweather bayan Azumi

Amir Khan
Image caption Amir Khan ya ce da azumi ba zai iya yin atisaye kamar yadda ya kamata ba

Dan Damben Birtaniya Amir Khan ya ce zai iya yin dambe da Floyd Mayweather a watan Satumba duk da cewar watan azumi zai kawo masa tsaikon atisaye.

Khan, mai shekaru 28, musulmi ne wanda ke shirin yin azumi da za a fara daga tsakanin farkon watan Yuni zuwa tsakiyar Yulin wannan shekarar.

Dan damben ya ce Mayweather yakan yi wasa ne a farkon Satumba wanda a lokacin ba a dade da kammala azumin ba.

Khan zai kara da Chris Algeri ranar 29 ga watan Mayu, ya kuma ce manajan Mayweather ke ta yin kokarin su fafata, tun nasarar da suka samu a kan Manny Pacquiao.

Mayweather, mai shekaru 38, dan Amurka ya lashe dukkan wasanni 48 da ya yi, kuma yana fatan ya buga karawa ta karshe a watan Satumba mai zuwa.