'Kwallon kafar mata na tafiyar hawainiya'

Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cikin watan Mayu za a zabi sabon shugaban hukumar kwallon kafa na duniya

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya ce wasannin kwallon kafar mata ba ya samun wani ci gaba idan aka kwatanta da na tamaular maza.

Shugaban ya ce ana samun tsaiko dangane da tagomashin wasannin da kuma daukar nauyin tamaular mata.

Blatter, mai shekaru 79, ya kara da cewar kwallon kafa motsa jiki ne, saboda haka ya bukaci gwamnatoci su nada mata a manyan mukaman da za su jagoranci kwallon kafa.

An zargi shugaban a shekarar 2004 da yunkurin tursasa wa 'yan kwallo mata saka matsastsun kaya domin wasan ya yi farin jini.

Blatter, wanda yake bukatar a sake zabensa shugaban Fifa karo na biyar, ya ce ya kamata a kawo sauyi a hukumar domin bai wa mata gurbin shiga kwamitin gudanarwar hukumar.

A shekarar 2013 ne aka zabi Lydia Nsekera ta Burundi mace ta farko da ta shiga cikin kwamitin gudanarwar Fifa.