Arsenal za ta ci moriyar Walcott — Wenger

Theo Walcott Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Arsenal tana mataki na uku a kan teburin Premier bana

Arsene Wenger ya kididdide yadda za su ci moriyar ganiyar shekarun Theo Walcott, yayin da yake fatan dan wasan zai amince ya tsawaita zamansa a Arsenal.

Saura shekara daya ya rage yarjejeniyar Walcott ta kare da Arsenal wanda ake rade-radin cewar zai koma taka leda a kulob din Liverpool.

Dan kwallon, mai shekaru 26, wanda yake murza leda daga gefan fili ta gaba zai iya koma wa tsakiya a matsayin mai cin kwallo in ji Wenger.

Wenger ya kara da cewa "lokacin da dan wasa ke tsakanin shekaru 26 zuwa 32 lokacin ne yafi kwazo sosai a matsayin mai cin kwallo, saboda haka ba mu son mu rasa shi a yanzu".

Arsenal tana fatan Walcott wanda ya ci kwallaye 72 a raga daga cikin wasanni 297 da ya yi zai bi sahun Thierry Henry wajen yawan cin kwallaye a raga a wasannin Arsenal.