Chelsea da Liverpool sun tashi wasa 1-1

Chelsea Liverpool
Image caption Mourinho ya dauki kofin Premier uku tare da Chelsea

Chelsea ta tashi wasa da Liverpool kunnen doki a gasar Premier wasan mako na 36 da suka yi a Stamford Bridge ranar Lahadi.

Chelsea ce ta fara zura kwallo a ragar Liverpool ta hannun kyaftin John Terry, yayin da Liverpool ta farke kwallon ta hannun kyaftin Steven Gerrard.

Chelsea wacce tuni ta dauki kofin Premier bana tun a makon jiya, bayan da ta doke Crystal Palace da ci daya mai ban haushi ta hada maki 84, kuma saura wasanni biyu a kammala gasar.

Liverpool kuwa tana mataki na biyar a kan teburi da maki 62, bayan da ta buga wasanni 36, za kuma ta kara da Crystal Palace a Anfield ranar Asabar.