Gasar Premier Nigeria wasannin mako na 8

Nigerian League week 8 fixtures Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Wasanni 10 za a buga a gasar Premier mako na 8

Enyimba International za ta karbi bakuncin Giwa FC a garin Aba a ci gaba da wasannin cin kofin Premier Nigeria gasar mako na 8 ranar Asabar.

Sauran wasannin da za a fafata El-Kanemi Warriorts za ta ziyarci Lobi Stars, sai Akwa United da Wikki Tourist da kuma karawa tsakanin Sunshine Stars da Shootings Stars.

Kano Pillars mai rike da kofin za ta karbi bakuncin Sharks a jihar Kano, a inda Bayelsa United za ta yi gumurzu da Dolphins da kuma wasa tsakanin Abia Warriors da Kwara United.

Ga jaddawalin wasannin mako na 8 da za a buga:

  • FC Taraba vs Gabros FC
  • Enyimba vs Giwa FC
  • Bayelsa Utd vs Dolphins
  • Lobi Stars vs El-Kanemi Warriors
  • Akwa Utd vs Wikki
  • Rangers vs Heartland
  • Sunshine Stars vs Shooting Stars
  • Warri Wolves vs Nasarawa Utd
  • Abia Warriors vs Kwara Utd
  • Kano Pillars vs Sharks