Kano Pillars ta ci Sharks kwallaye 2-0

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Sakamakon wasannin mako na 8 a gasar Premier Nigeria

Kano Pillars ta doke Sharks da ci 2-0 a gasar Premier wasannin mako na takwas da suka yi a ranar Lahadi a jihar Kano.

Pillars ta ci kwallon farko ta hannun Ezekiel Mbah a minti na biyar da dawo wa daga hutu, yayin da Adamu Hassan ya ci ta biyu saura minti bakwai a ta shi daga karawar.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Lobi Stars da El-Kanemi Warriors sun tashi wasan babu ci, haka karawa tsakanin Enyimba da Giwa FC suka tashi duro.

Fafatawar da aka yi tsakanin Bayelsa United da Dolphin tashi suka yi 2 - 2, yayin da Sunshine Stars ta ci 3SC kwallaye 2-0.

Ga sakamakon wasannin mako na 8 da aka yi:

  • Lobi Stars 0-0 El-Kanemi
  • Abia Warriors 2-0 Kwara Utd
  • Enyimba 0-0 Giwa FC
  • Bayelsa United 2 - 2 Dolphins
  • Sunshine Stars 2-0 Shooting
  • Akwa United 0-0 Wikki
  • FC Taraba 3-3 Gabros
  • Rangers 1-0 Heartland
  • Warri Wolves 4-1 Nasarawa