Canjaras zai kawo wa Madrid tsaiko a La Liga

Madrid Valencia Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid za ta karbi bakuncin Juventus a gasar zakarun Turai wasa na biyu

Tashi wasa 2-2 da Real Madrid ta yi da Valencia a gasar cin kofin La Liga wasan mako na 36 da suka yi ranar Asabar zai iya kawo mata tsaikon lashe kofin bana.

Valencia ce ta fara zura kwallaye biyu a ragar Madrid ta hannun Paco Alcacer da Javier Fuego Martinez tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Daf da za a tafi hutu Ronaldo ya zubar da fenariti, kuma bayan an dawo daga hutu ne Madrid din ta farke kwallayenta biyu ta hannun Kepler Laveran Pepe da kuma Francisco Alarcon Suarez

Bayan da Ronaldo ya barar da fenaritin, sau uku Madrid ta buga kwallo tana dukan turke kuma da wannan sakamakon Barcelona ta bai wa Madrid tazarar maki hudu.

Barcelona ta doke Real Sociedad 2-0 a wasan da suka yi ranar Asabar, kuma idan Barca ta ci wasa daya daga cikin wasanni biyu da suka rage ta dauki kofin La Ligar bana.

Madrid ta tsinci kanta cikin wannan halin ne bayan da ta samu nasara a wasa daya daga cikin wasanni shida da ta yi da kungiyoyin dake matsayin hudun farko a teburin La Liga.

Za a tsaida wasannin kasar Spaniya ranar 19 ga watan Mayu sakamakon takaddama tsakanin hukumar kwallon kafar kasar da gwamnati kan raba kudin nuna wasanni a talabijin.