Kotu za ta saurari tsayar da wasannin Spaniya

La Liga strike Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 19 ga watan Mayu ne za a dakatar da dukkan wasannin kasar Sipaniya

Kotun Spaniya ce za ta yanke hukunci a ranar Laraba idan dakatar da wasannin kwallon kafa a kasar na kan ka'ida ko kuma akasin hakan.

Hukumar kwallon kafar Spaniya ce (RFEF) ta ce ta dakatar da wasannin gasa a kasar, a ranar 19 ga watan Mayu, inda ita ma kungiyar 'yan wasa ta ce za ta mara baya kan takaddamar hakkin nuna wasanni a talabijin.

Hakan kuma zai kawo tsaiko ga sauran wasannin cin kofin La Liga biyu da suka rage na bana da kuma wasan karshe na cin Copa del Rey.

Hukumar kwallon kafar kasar da kungiyar 'yan wasa ba su amince da dokar da ta bai wa hukumar gudanar da gasar La Liga tara kudade da raba wa kungiyoyi hakkin nuna wasanninsu a talabijin ba.

A rabon da ake yi a yanzu Real Madrid da Barcelona ne suka fi karbar kaso mafi tsoka daga ciki.

Ranar Laraba ce kotun za ta fara sauraren takaddamar tsakanin hukumar kwallon kafar kasar da kuma hukumar dake kula da gasar La Liga.