'Za mu fanshe wasanmu da Barcelona'

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Pep Guardiola na fuskantar matsin lamba a Bayern Munich

Bayern Munich za ta yi iyaka kokarinta har zuwa karshe domin ganin ta fanshe kwallaye ukun da Barcelona ta zura mata a gasar zakarun Turai.

Ko a bugun gabda na kusada karshe ma, FC Porto ta samu galaba a kan Bayern da ci uku da daya a Portugal, amma da suka je Jamus, sai aka lallasa Porto da ci shida da day.

Kocin Bayern, Pep Guardiola ya ce "Ta yadda za mu samu nasara ka wai shi ne mu murza leda fiye da Barcelona daga farko har karshe."

Manyan 'yan wasan Bayern, Franck Ribery da Arjen Robben ba za su buga wasan ba saboda rauni.

Barcelona na da burin lashe kofuna uku a kakar wasa ta bana watau na La Liga da Copa del Rey da kuma na zakarun Turai.