Schalke ta dakatar da Boateng da Sam

Kevin-Prince Boaten Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Schalke ta ce 'yan wasan biyu za su iya neman wata kungiyar

Kungiyar Schalke ta dakatar da Kevin-Prince Boateng da Sidney Sam nan take, bayan da Colongne ta doke ta da ci 2-0 a ranar Lahadi.

Boateng, mai shekaru 28, dan kasar Ghana ya buga mintina 59 a wasan da aka cinye su, wanda Sam, dan kasar Jamus, bai buga fafatawar ba.

Kociyan Schalke Roberto Di Matteo ya bayyana 'yan wasan biyu da rashin mutunta juna, a inda ya ce za su iya komawa wata kungiyar taka leda.

Shi kuwa mai yi wa Schalke wasan tsakiya Marco Hoger, wanda ya buga karawar da Cologne an dakatar da shi mako guda.

Hoger, mai shekaru 25 ya koma Schalke taka leda daga Alemannia Aachen ne a shekarar 2011.

Schalke ta dauko Sam daga Bayern Leverkusen a bara kan kwantiragin shekaru hudu, yayin da ta sayo Boateng daga AC Milan a shekarar 2013 kan yarjejeniyar shekaru uku.