Swansea ta ci Arsenal 1-0 a Emirates

Arsenal Swansea
Image caption Arsenal tana mataki na uku a teburin Premier da maki 70

Swansea ta ci Arsenal kwallo daya mai ban haushi a gasar Premier da suka yi ranar Litinin a filin wasa na Emirates.

Bafetimbi Gomis ne ya ci kwallon da kai sauran minti biyar a tashi wasa daga bugun da Jefferson ya yi wo masa.

Da wannan sakamakon Swansea ta takawa Arsenal burkin yawan lashe wasanni 11 da ta yi a jere.

Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na uku a teburin Premier yayin da Manchester City wacce ke mataki na biyu a teburin ta ba ta tazarar maki uku tsakani.

Arsenal za ta ziyarci Manchester United a gasar Premier ranar Lahadi a Old Trafford.