An rufe zaben gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC

WFOY
Image caption Ranar 26 ga watan Mayu za sanar da wacce ta lashe kyautar bana

An rufe kada kuri'ar zaben gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta bana da BBC za ta karrama, a inda za a sanar da sunan wacce ta lashe kyautar a ranar 26 ga watan Mayu.

Cikin 'yan kwallo biyar da suke yin takarar sun hada da 'yar kwallon Sipaniya Veronica Boquete da 'yar wasan Jamus Nadine Kessler da Kim Little ta Scotland da Mata ta Brazil da 'yar kwallon Nigeria mai taka leda a Liverpool Asisat Oshoala.

Kyautar ita ce karo na farko da wata kafar yada labarai ta duniya za ta yi.

Masana wasan kwallon kafa da suka hada da 'yan jaridu da masu horar da tamaula da kuma tsoffin 'yan wasa ne suka fitar da 'yan wasa biyar da babu kamar su a bana a cikin watan Afirilu.

Za a sanar da wacce ta lashe kyautar bana ne a shirin BBC World Service.