Eja din Bale ya cika surutai — Ancelotti

Ancelotti Bale
Image caption Real Madrid za ta karbi bakuncin Juventus ranar Laraba a kofin zakarun Turai

Carlo Ancelotti ya shaida wa eja din Gareth Bale ya daina yawan magana, bayan da ya ce 'yan wasan Madrid ba sa taimakon dan wasan.

Jonathan Barnett ya ce Bale yana fama da jin radadin rashin samun karfin gwiwa daga abokan wasansa.

Anceloti ya ce "Muna cikin wata duniya mai dunbin al'umma da wani lokacin wasu ke sha'awar yin maganganu barkatai".

Bale ya ci kwallaye 24 daga wasanni 46 tun komawarsa Madrid a bara, yayin da ya taimaka mata lashe kofin zakarun Turai da kuma Copa del Rey.

Sai dai kuma yana shan kalubale daga wajen wasu magoya bayan Madrid a bana da kuma wasu 'yan jaridar Spaniya.

Haka kuma an yi ta sukar Bale wanda ya ci wa Madrid kwallaye 15 a bana cewar bai taka leda a karawar da Juventus ta doke Madrid ba.