Farashin tikitin kallon wasan Gerrard na karshe ya karu

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steven Gerarrd ya buga wa Liverpool wasanni 502 ya kuma ci kwallaye 119.

Farashin tikitin kallon wasan karshe da Steven Gerrard zai buga wa Liverpool tamaula a Anfield ya yi tashin gwauron zabi, a inda ya kai £1,300.

A ranar talata farashin da ake sayar da tikitin wasan Liverpool da Crystal Palace a intanet ya fara daga £100 zuwa £1,324.64.

Liverpool za ta fafata da Crystal Palace a gasar Premier gasar mako na 37 ranar Asabar kuma shi ne wasan karshe da kyaftin Gerrard zai yi da Liverpool a Anfield.

Gerrard, mai shekaru 34 wanda ya buga tamaula a Liverpool shekaru 17, zai yi bankwana da kulob din a makon gobe bayan sun yi wasa da Stoke City, a inda zai koma buga gasar Amurka.

Farashin tikitin kallon wasa a karamin bene a filin Anfield ana sayar da shi ne daga kan kudi £47.