Ashley ya bukaci a biya shi bashin da yake bi

Mike Ashley Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mike Ashley na damar nada daraktoci biyu a kulob din Rangers

Mai Newcastle United Mike Ashley ya bukaci hukumar gudanarwar Rangers da ta kira taron masu hannun jari, domin a biya shi bashin fan miliyan 5 da ya ke bin su.

Ashley, mai rike da kaso 9 na hannun jarin Rangers ya bukaci hukumar da ta yi masa bayanin da yasa aka cire kulob din daga kasuwar hannun jari ta AIM.

Idan aka biya shi bashin zai bai wa Rangers damar dawo da hakkinsa na mallakar wurin da suke gudanar da atisaye da tallace-tallace da kuma sauran harkokin kasuwanci.

Wadannan bukatu na Ashley sun biyo bayan da Dave King dan asalin Africa ta kudu ya maye gurbin tsohon daraktan wasannin Rangers.

Yanzu haka ana jiran amincewar hukumar kwallon kafar Scotland ta yarda da nada sabon shugaban.