An dakatar da Ancelotti wasannin La Liga biyu

Carlo Ancelotti Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Ancelotti ba zai jagoranci sauran wasanni biyu da Madrid za ta yi a La Liga ba

Hukumar gudanar da gasar La Liga ta dakatar da Carlo Ancelotti jagorantar Real Madrid wasanni biyu, sakamakon kalubalantar alkalin wasa da ya yi.

Alkalin wasa Carlos Clos Gomez ne ya rubuta rahoton cewar Ancelotti ya yi masa gatse da kuma tafi a lokacin da suka tashi wasa 2-2 da Valencia.

Hakan na nufin Ancelotti, mai shekaru 55, ba zai jagoranci Madrid sauran wasanni biyu da suka rage na gasar La Ligar bana ba.

A rahoton alkalin wasa Carlos ya kuma ce Ancelotti ya kuma ci gaba da yin tafi da mataimakin alkalin wasa a lokacin da aka shiga hanyar fita daga filin wasa.

Dokar hukumar kwallon kafar Spaniya ta ce idan koci ya raina alkalin wasa ko yin watsi da hukunci za a iya dakatar da shi wasanni tsawon wata daya.