Guardiola: Lionel Messi tamkar Pele ne

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lionel Messi tamkar Pele ne- Inji Guardiola.

Kociyan Bayern Munich, Pep Guardiola, ya kwatanta Lionel Messi da Pele na Brazil a lokacin da yake nuna goyon bayansa ga tsohon kulob din sa na Barcelona bayan ya kai zagayen karshe na cin a gasar zakarun Turai.

Messi ne ya sa Barca ta ci 3 da 0 a karawar farko da suka yi, cin da Bayern ta kasa fanshewa, duk da ramuwa cin 3 da 2 da ta yi a karawar su ta biyu.

"Dan wasan kwararre ne na kowanne lokaci, ina kwatanta shi da Pele," in ji Guardiola mai shekaru 44.

"Ina fata Baca za su ci gasarsu ta championship league karo na biyar kuma na karshe."

Barca za su kara da Real Madrid ko Juventus a Berlin a ranar 6 ga watan Yuni.

Dan gaban Brazil Nyemar ya ci sau biyu a filin wasa na Allianz a inda suka lallasa zakarun Turai Spania da ci 5-1 kafin 'yan Bayern din su rama a wanan daren.

Amma Guardiola ya ci gaba da yabon Messi wanda ya ceto kulob din a zagayen kusa da na karshe a Nou Camp a makon da ya wuce.

Messi ya ci kwallaye 53 a kakar wasa ta bana, kari a kan 44 da gasar bara bayan shawo kan matsalolin zargin kin biyan haraji da rauni da ya ji.

A tsawon lokacin da yake Barcalona dai Guradiola da Messi sun ci kofa-kofai 14 tsakanin 2008 da 2012.