Guardiola ya kwatanta Messi da Pele

Messi Guardiola Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lionel Messi ya ci kwallaye 53 a kakar wasannin bana

Kociyan Bayern Munich Pep Guardiaola ya kwatanta Lionel Messi da tsohon zakaran kwallon kafa na duniya Pele, a inda ya yi fatan Messi zai lashe kofin zakarun Tura a bana.

Messi ne ya jagoranci Barca ta doke Munich da ci 3-0 a wasan farko da suka yi a Spaniya, kafin Bayern Munich ta ci Barcelona 3-2 a ranar Talata.

Guardiola ya ce "Shi ne dan kwallon da yafi yin fice a duniya, kuma ina kwatantashi da Pele, ina mai fatan ya dauki kofin zakarun Turai na bana".

Barcelona wacce ta kai wasan karshe a kofin bana za ta buga da wacce ta samu nasara tsakanin Real Madrid da Juventus wadan da za su kara a ranar Laraba.

Messi ya ci kwallaye 53 a gasar bana, a inda ya dora a kan kwallaye 44 da ya zura a raga a bara duk da fama da yin jinya da ya sha.