Mahaifiyar Falcao ta ce zai iya barin United

Radamel Falcao Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya koma wasa aro a United ne a watan Satumbar bara

Mahaifiyar Radamel Falcao ta ce danta ba ya farin ciki da halin da ya tsinci kansa a Manchester United zai kuma iya barin kulob din a bana.

Dan kasar Colombia, ya koma United ne buga wasa aro daga Monaco a watan Satumba, a inda ya ci kwallaye hudu cikin wasanni 28 da ya yi.

Falcao, mai shekaru 29, ya buga wa United wasa daya daga cikin wasanni takwas da ta yi a baya, tun daga wanda Chelsea ta doke ta 1-0.

Kafin ya koma United buga tamaula yana daga cikin fitattun 'yan wasa masu cin kwallo, a inda ya zura kwallaye 104 daga cikin wasannin 139 da ya yi a Porto da Atletico Madrid da Monaco.

Dan kwallon ya gamu da cikas bayan da ya ji rauni a watan Janairu wanda ya hana shi buga gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil.