Mourinho ya aika min sako — Schurrle

Andre Schurrle Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasanni 14 Andre Schurrle ya buga wa Chelsea a farkon kakar wasan bana

Tsohon dan kwallon Chelsea Andre Schurrle ya ce ya samu sako ta wayar salularsa daga Jose Mourinho a inda ya yi masa albishir cewa ya lashe lambar zinariya ta Premier.

Schurrle, mai shekaru 24, ya koma Wolsburg ta Jamus daga Chelsea kan kudi fam miliyan 22 a watan Satumba.

Dan kwallon Jamus din, ya buga wa Chelsea wasanni 14 kuma a sauyin dan wasa.

Schurrle ya shaida wa BBC cewar bai yi tunanin zai samu lambar yabo ba ta daukar kofin Premier da Chelsea ta yi, bayan da bai buga wasanni da dama ba a kulob din.

Ya kuma ce Mourinho ne ya tura masa sako ta salula da yi masa albishir, sannan ya gayyace shi wasan karshe, kuma abin farinciki ne a wajensa.