Chelsea ta dauko dan kwallon Brazil Nathan

Nathan Allan de Souzahas Hakkin mallakar hoto chelsea fc
Image caption Nathan ya ci kwallaye 5 a wasanni 5 da ya yi a gasar cin kofin duniya ta matasa shekaru 17 a 2013

Chelsea ta dauko dan kwallon Brazil Nathan mai buga tamaula a kulob din Atletico Paranaense, sai dai ba ta bayyana kudin da ta sayo dan wasan ba.

Dan kwallon, mai shekaru 19, zai koma murza leda a Stamford Bridge ranar 1 ga watan Yuni, idan likitocin kulob din sun kammala duba lafiyarsa.

Cikakken sunan dan wasan shi ne Nathan Allan de Souzahas, kuma ya wakilci tawagar kwallon kafar Brazil ta matasa 'yan kasa da shekaru 17 da kuma ta 20.

Nathan ya bi sahun 'yan kwallon Brazil da suka koma Chelsea taka leda da suka hada da Ramires da Willian da Oscar da kuma Filipe Luis.

Haka kuma Chelsea tana da matasan 'yan wasan Brazil da suka hada da Wallace da Lucas Piazon da ta bayar da su ga wasu kungiyoyin wasa aro.