Dnipro da Sevilla sun kai wasan karshe a Europa

Dnipro FC
Image caption Sevilla da Dnipro za su buga wasan karshe ranar 27 ga watan Mayu a Warsaw

Dnipro za ta kara da Sevilla mai rike da kofin zakarun Turai wato Europa, bayan da ta doke Napoli da ci daya mai ban haushi a karawar da suka yi a ranar Alhamis.

Yevhen Seleznyov ne ya ci wa Dnipro kwallon, wanda ya kawo karshen yawan wasanni 10 da Napoli ta yi, kuma Dnipro ta ci Napoli kwallaye 2-1 a karawar da suka yi jumulla.

Ita kuwa Sevilla ta kai wasan karshen ne bayan da ta doke Fiorentina da ci 2-0 a Italiya, kuma jumulla ta ci kwallaye 5-0 kenan.

Kungiyoyin biyu za su kara ne a wasan karshe da za su yi ranar 27 ga watan Mayu a Warsaw.