Manchester United ta yi hasarar £2.9m

Old Trafford Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manchester United za ta kara da Arsenal a gasar Premier ranar Lahadi a Old Trafford

Manchester United ta ce ta yi hasarar £2.9m a farkon watanni uku na kakar bana, bisa raguwar kudaden nuna wasanninta a talabijin da kuma na shiga kallon wasa.

United ta yi hasarar £2.9m tsakanin watannin Janairu zuwa Maris, duk da cewa an kwatanta ribar £11m a tsakanin wadannan watannin.

Asarar da United ta yi zai kara mata matsi a kan bashin da ake binta, wanda zai karu zuwa kaso 12 cikin 100 da zai kai £395.4m.

Koda yake United din ta bunkasa tsarin samun kudadenta a shekarar 2015.

Ana hasashen kungiyar za ta samu £103m zuwa £110m a watan Yunin 2015, idan aka kwatanta da hasashen da aka yi cewar za ta samu £90m zuwa £95m a baya.

Haka kuma hannun jarin Manchester United ya karu zuwa kaso daya da digo 16 cikin dari.