Na yi takaicin rashin lashe kofin Premier - Gerrard

Steven Gerrard
Image caption Gerrard ya fara wasa a Liverpool a shekarar 1998 ya kuma buga wasanni 502 ya ci kwallaye 119

Kyaftin din Liverpool mai barin gado Steven Gerrard ya ce ya yi takaici da bai lashe kofin Premier ba a tsawon wasannin da ya buga a Anfield.

Gerrard, mai shekaru 34, zai buga wasan karshe a Anfield a karawar da Liverpool za ta yi da Crystal Palace a gasar Premier wasan mako na 37.

Dan kwallon zai koma murza leda a gasar Amurka da kulob din LA Galaxy a watan Yuni mai zuwa.

Gerrard ya ce ya yi takaici da bai lashe kofin Premier ba, ba shi kadai bane takaicinsa a zaman da ya yi da Liverpool, amma yafi jin takaici da bai dauki Premier ba.

Ga jerin kofunan da Gerrard ya dauka a Liverpool:

  • FA Cup: 2001, 2002, 2006
  • Football League Cup: 2001,2003, 2012
  • FA Community Shield: 2006
  • UEFA Champions League: 2005
  • UEFA Cup: 2001
  • UEFA Super Cup: 2001,2005