An kori Boca Juniors daga Copa Libertadores

River Plates Players Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dade ana samun yamutsi a lokacin wasanni a kasar Argentina

An kori kulob din Boca Juniors na Argentina daga gasar Copa Libertadores, bayan da magoya bayanta suka fesa wa 'yan kwallon River Plate wani abu mai ya ji a ranar Alhamis.

Haka kuma an ci tarar Boca kudi US$200,000, sannan za ta yi wasanni hudu a gida ba tare da 'yan kallo ba.

A karawar sai da aka kai 'yan wasan River Plate hudu asibiti, sakamakon shakar iska mai yaji da magoya bayan Boca suka fesa a filin Bombonera a lokacin da aka tafi hutu.

An kuma kara hukunta Boca Juniors da cewar ba za ta buga wasanni hudun da za ta yi a waje ba.

A saboda haka River Plate ta kai wasan daf da karshe kenan a gasar wacce ke dai-dai da gasar cin kofin zakarun Turai, kuma za ta fafata da Cruzeiro ta Brazil.

An dade ana samun rikici a wasannin kwallon Argentina, a inda cikin watan Disamba aka jefi dan wasa Franco Nieto a kai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa.