Man United da Arsenal sun tashi wasa 1-1

Walcott Blakett
Image caption Manchester United da Arsenal sun raba maki daya-daya a tsakaninsu

Manchester United ta tashi wasa kunnen doki tsakaninta da Arsenal a gasar cin kofin Premier wasan mako na 37 da suka buga a Old Trafford ranar Lahadi.

Ander Herrara ne ya fara ci wa United kwallo a raga kafin a tafi hutun rabin lokaci, bayan da aka dawo daga hutu Tyler Blackett ya ci gida daga bugun da Theo Walcott ya yi.

Haka kuma a fafatawar tsohon golan Barcelona Victor Valdes ya fara yi wa United wasansa na farko a Old Trafford tun lokacin da ya koma can, bayan da ya canji David De Gea wanda ya ji rauni a karawar.

Da wannan sakamakon United ta ci gaba da zama a mataki na hudu a teburin Premier da maki 69, za kuma ta ziyarci Hull City a wasan karshe ranar Lahadi.

Arsenal kuwa tana matsayinta na uku a kan teburi, za kuma ta buga kwantan wasa da Sunderland ranar Laraba, sannan ta karbi bakuncin West Brom ranar Lahadi a Emiraters.