Pillars ta kwaso maki uku a Abia

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Da wannan nasarar Kano Pillars ta hada maki 15 kenan

Kungiyar Kano Pillars ta ci Abia Warriors kwallo daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na tara da suka buga a Umuahia ranar Lahadi.

Pillars wacce take rike da kofin Premier ta ci kwallonta ne ta hannun Adamu Hassan a minti na hutu da fara wasa.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Enyimba ta ci Dolphins har gida da ci 2-1, karawa tsakanin El-Kanemi Warriors da Bayelsa ta shi suka yi babu ci a tsakaninsu.

Ita ma Nasarawa United da ci daya mai ban haushi ta doke Sunshine Stars, yayin da aka tashi karawa tsakanin Wikki Tourist da Lobi Stars babu ci.

Ga sakamakon wasannin mako na tara da aka yi:

  • Gabros FC 0-0 Sharks
  • Giwa FC 0-0 FC Taraba
  • Dolphins 1-2 Enyimba
  • El-Kanemi Warriors 0-0 Bayelsa United
  • Wikki Tourists 0-0 Lobi Stars
  • Heartland 2-0 Akwa United
  • Shooting Stars 1-1 Rangers
  • Nasarawa United 1-0 Sunshine Stars
  • Abia Warriors 0-1 Kano Pillars