Ayew ne fitatcen dan kwallon Afirka a Faransa

Andre Ayew Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ayew ya koma Marseille a shekarar 2007

Dan kwallon Ghana mai taka leda a kulob din Marseille na Faransa ya lashe kyautar dan wasan Afirka da yafi yin fice a gasar Faransa a bana.

Ayew mai shekaru 25, ya doke wadan da suka yi takara da suka hada da Max-Alain Gradel na Ivory Coast's (Saint-Etienne) da kuma Aymen Abdennour na Tunisia (monaco).

An kuma bai wa Ayew kofin Marc-Vivien Foe a matsayin tukucin lashe kyautar da ya yi, kuma ana hangen kyautar karshe da zai karba a Marseille, yayin da zai bar kulob din a badi.

Ayew ya ci kwallaye 10 daga cikin wasanni 27 da ya buga wa kulob din a kakar wasannin bana.

Ga jerin wadan da suka lashe kyautar Marc-Vivien Foe a baya

2014: Vincent Enyeama (Nigeria/Lille)

2013: Pierre-Emerick Aubameyang (Gabon/Saint-Étienne)

2012: Younès Belhanda (Morocco/Montpellier Hérault SC)

2011: Gervinho (Ivory Coast/Lille)

2010: Gervinho (Ivory Coast/Lille)

2009: Marouane Chamakh (Morocco/Bordeaux)