Fyade: Tsohon zakaran Tennis zai sha dauri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bob Hewitt

An yanke wa wani tsohon zakaran wasan Tennis, Bob Hewitt hukunci daurin shekaru shida a gida yari, bayan da wata kotu da ke Afirka ta kudu ta same shi da laifin yi wa wata yarinya karama fyade.

Matar Hewitt ta nemi sassauci a kan hukuncin da kotu ta yanke wa mijin,bisa laifin da ya aikata shekaru 30 da suka wuce.

Mai sharia a baban kotu da ke Pretoria, Bert Bam ya samu Bob Hewitt da laifi na rashin nuna nadama a lokacin shari'ar kuma ya ce ya kamata a tabbatar da adalci a kan duk wani wanda ya aikata laifi koda mai yawan shekaru ne a duniya.

Tsohon dan wasan tennis din, wanda ya taba rike kambun gasar, ya musanta aikata laifin, inda ya bukaci kotun ta yi masa sassauci saboda shekarun sa.

Dan shekaru 75, Bob Hewitta ana tuhumarsa ne da aikata fyade da kuma cin zarafin mata a shekarun 1980 da kuma 1990, a lokacin da ya koyawa wasu yara mata kanana wasan Tennis.