Qatar 2022: Shin wane hali leburori ke ciki ?

Qatar Labourers Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dubban 'yan kasar Afirka ta Kudu ne ke aikin gina filayen wasannin a Qatar

Kamfanonin da suke daukar dawainiyar gasar cin kofin duniya sun bukaci a ba su bayani kan halin da leburorin da ke gina filayen wasanni ke ciki a Qatar.

An yi kakkausar suka kan yanayin wurin aiki da gidajen da leburori bakin haure ke kwana wadanda suke aikin gina filayen wasanni.

Shugaban kungiyar kasuwanci ta duniya, Sharan Burrow ya ce yana yin da ma'aikata ke gudanar da aikin tamkar bautar bayi ne.

An aike da wasiku zuwa manyan kamfanoni takwas da suke daukar nauyin gasar cin kofin duniya, da su yi amfani da matsayinsu su saka wa Fifa matsin lamba kan batun.

Kamfononin sun hada da Adidas da Gazprom da Hyundai da Kia da McDonald da Budweiser da Coca-Cola da kuma Visa.

Ko a bara sai da kamfanonin suka yi wa Fifa matsin lamba kan sanin takamaiman dalilan da Fifa ta bai wa Qatar damar karbar bakuncin kofin duniya na shekarar 2022.