Wenger ya yi shiru kan batun dauko Sterling

Raheem Sterling Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Tun a baya dan wasan ya ki ya tsawaita kwantiragi a Liverpool

Arsene Wenger ya ki ya ce komai kan idan zai dauko Raheem Sterling zuwa Arsenal a badi ko kuma akasin haka.

Ana kyautata zaton Sterling, mai shekaru 20, zai nemi izinin barin Liverpool a wajen koci Brendan Rodgers.

Wenger ya ce "A badi za mu bukaci dauko 'yan wasa, amma a wannan lokacin bama cikin yanayin tattauna wa kan batun".

Arsenal za ta kara da Sunderland a kwantan wasan gasar Premier ranar Laraba, domi neman gurbin mataki na uku a gasar.

Haka kuma Arsenal din za ta nemi lashe kofin kalubale, a inda za ta fafata da Aston Villa ranar 30 ga watan Mayu a Wembley.