Ross Wallace zai bar Burnley

Ross Wallace Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Burnley za ta koma buga gasar Championship a badi

Kulob din Burnley zai kawo karshen zaman Ross Wallace da shi a karshen kakar bana, yayin da zai ci gaba da rike Micheal Duff a shekara ta 12 a jere a Turf Moor.

Wallace, mai shekaru 29, ya yi wa Burnley wasanni 18 a kakar Premier ta bana, a inda Duff ya yi mata wasanni 22, kafin kulob din ya bar buga Premier zuwa Championship a badi.

Duff, mai tsaron baya ya buga wa Burnley wasanni sama da 350 tun lokacin da ya koma can kan kudi £30,000 a shekarar 2004.

Tuni Steven Reid ya sanar da cewar zai yi ritaya a karshen kakar wasan bana, yayin da Danny Ings zai bar kulob din.