Ramsey zai ci gaba da jan ragamar QPR

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption QPR ta kulla yarjejeniyar shekaru uku da Chris Ramsey a matsayin kocin kulob din.

QPR ta kulla yarjejeniyar shekaru uku tare da Chris Ramsey a matsayin kocin kulob din.

An bai wa Ramsey mai shekaru 53, aikin a karshen watan Fabrairu ne, bayan murabus din da Harry Redknapp ya yi.

Shugaban kulob din Tony Fernandes, ya ce " Chris ya karbi aikin lokacin da muke cikin wani mawuyacin hali".

QPR ta samu nasara a wasanni 3 cikin 14 da Ramsey ya jagoranta, kuma za su shiga wasan su na karshe a Leicester daga kasan tebur da bambancin ci daya.

Fernandes ya kara da cewa "Rayuwar sa gaba ki daya lura da kulob ne da aikin manajan kulob, kuma na tabbata zai inganta kuma za mu dawo da martabarmu."