An rage hukuncin da aka yanke wa Fabregas

Cesc Fabregas Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Cesc Fabregas ya taka rawar gani a Chelsea a kakar wasannin bana

Hukumar kwallon kafar Ingila ta rage hukuncin dakatar da Cesc Fabregas daga buga wasanni uku zuwa wasa daya, bayan da aka bashi jan kati a wasan da suka yi da West Brom.

An kori Fabregas ne a karawar da West Brom ta doke Chelsea 3-0 a ranar Litinin, bayan da ya nuna halin rashin da'a, yayin da ya buga kwallo ta bugi kan Chris Brunt daga yadi na 20.

Hukuncin aikata laifin dai shi ne dakatarwa daga buga wasanni uku, amma Chelsea ta yi korafin cewar hukuncin ya yi tsauri.

Rage masa hukuncin da aka yi ya sa Fabregas ba zai buga wasan karshe na Premier bana ba da Chelsea za ta yi da Sunderland a ranar Lahadi a Emirates.

Tuni dai Chelsea ta dauki kofin Premier na bana tun lokacin da ya rage saura wasanni uku a kammala gasar, kuma kofi na biyar da ta dauka jumulla kenan.