Kano Pillars ta ci Gabros kwallaye 2-1

Kano Pillars Hakkin mallakar hoto kanopillarsweb
Image caption Za a ci gaba da wasannin gasar Premier a ranar 14 ga watan Yunin 2015

Kano Pillars mai rike da kofin gasar Premier ta doke Gabros International da ci 2-1 a wasan mako na 10 da suka buga ranar Laraba.

Pillars din ce ta fara zura kwallo ta hannun Moses Ekpai a minti na 19 da fara wasa, sannan Rabi Ali ya kara ta biyu a raga a minti na 25 daga kwallon da Moses Ekpai ya bashi.

Ita kuwa Gabros ta zare kwallo daya ne ta hannun dan wasanta Nwosu Oluchukwu a minti na 17 da dawo wa daga hutun rabin lokaci.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi Enyimba ta casa Elkanemi Warriors da ci 3-1 a garin Aba, yayin da aka tashi wasa tsakanin Rangers da Nasarawa United babu ci.

Fafatawa tsakanin Sharks da Giwa FC tashi suka yi kunnen doki a garin Fatakwal, ita kuwa Lobi Stars ta doke Heartland da ci daya mai ban haushi.

Bayan da aka kammala wasannin mako na 10 a gasar za kuma ayi hutu zuwa ranar 14 ga watan Yuni kafin aci gaba da fafatawa.

Ga sakamakon wasannin da aka buga ranar Laraba:

Enyimba 3-1 El-Kanemi Warriors Kano Pillars 2-1 Gabros Akwa United 2-1 Shooting Stars Lobi Stars 1-0 Heartland Sunshine Stars 1-0 Kwara United FC Taraba 1-1 Dolphins Sharks 1-1 Giwa FC Rangers 0-0 Nasarawa United Bayelsa United 1-0 Wikki