PSG ta dara Man City wajen biyan albashi

Paris St Germain Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Paris St Germain ce ta lashe kofin gasar Faransa na bana

Paris St-Germain ta Faransa ta dara Mancheser City a matsayin kungiyar wasa da ta fi biyan 'yan wasanta albashi a duniya.

A wani bincike da aka gudanar a shafin tattara bayanan sirri a intanet ya nuna cewar PSG tana biyan matsakaicin albashin 'yan wasa da ke yi mata kwallo £101,898 a duk mako.

A bara, Manchester City ce ke kan gaba a inda matsakaicin albashin da take biya ya kai £96,445, amma yanzu ta koma mataki na uku, yayin da Real Madrid ce a matsayi na biyu.

Manchester United tana mataki na shida, Chelsea ce kuma ta bakwai, Arsenal ta goma a inda Liverpool ke mataki na 14 a binciken da aka yi.

An yi binciken ne kan kungiyoyi 333 daga gasar wasanni 1 a kasashe 13 da suka hada da kwallon kafa da Baseball da kwallon zari rugar Amurka da kwallon Kirket da kuma kwallon hokey ta kankara.

Gasar kwallon kwandon Amurka ce ta ci gaba da rike cmatsayin wacce aka fi biyan albashi mai tsoka, a inda matsakaitan 'yan wasanta ke karbar £2.67m a shekara.

Ga jerin kungiyoyin da suka fi biyan alabshi a duniya:

1: Paris St Germain (£101,898)

2: Real Madrid (£96,933)

3: Manchester City (£96,445)

4: Barcelona (£90,675)

5: Los Angeles Dodgers (£89,999)

6: Manchester United (£89,988)

7: Bayern Munich (£85,935)

8: Chelsea (£83,713)

9: New York Yankees (£81,992)

10: Arsenal (£77,963)