An yi wa Sterling ihu da zai karbi kyauta

Raheem Sterling Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Ana hasashen Sterling zai bar Liverpool a karshen kakar bana

Raheem Sterling ne ya lashe kyautar matashin dan wasan Liverpool da ya fi yin fice a bana, sai dai wasu magoya baya sun yi masa ihu a lokacin da zai karbi kyautar.

Dan wasan, mai shekaru 20, ya lashe kyautar ne sa'o'i 24 da ake hasashen zai nemi izinin barin Anfield a bana a wajen Brendan Rodgers.

Babban jami'in Liverpool, Ian Ayre da koci Brendan Rodgers da kuma Reaheem Sterling za su tattauna a ranar Juma'a domin lalubo bakin zaren.

An kuma zabi dan wasan Brazil Philippe Coutinho, mai shekaru 22, a matsayin dan kwallon da ya fi haskaka wa a kulob din a gasar kakar bana.

Liverpool za ta kammala gasar bana a mataki na biyar a gasar Premier, wanda hakan zai sa ba za ta buga gasar cin kofin zakarun Turai na UEFA Champions League a badi.

Kuma Brendan Rodgers ya zamo mai horar wa na farko da bai dauki kofi a Liverpool ba a shekaru ukun farko da ya yi a kulob din tun daga shekarar 1950.