Manyan kungiyoyin Turai na zawarcin Ayew

Andre Ayew Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ayew ne ya lashe kyautar dan kwallon Afirka da ya fi yin fice a Faransa a bana

Dan kwallon Ghana, Andre Ayew ya ce yana ta binciken kungiyar da zai zaba ya koma taka leda a tsakanin Ingila ko Italiya ko kuma Jamus da suke zawarcinsa.

Dan wasan, mai shekaru 25, zai bar wasa a Marseille ta Faransa a karshen kakar wasan bana, bayan da ya ki amincewa ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din.

Ayew ya shaida wa BBC cewar yana son ya koma buga gasar wata kasar da ban mai dunbin al'adu da yawa.

Idan Ayew ya bar Marseille zai kawo karshen zumuncin shekaru 28 da kulob din ya yi da iyalan gidansu.

Mahaifinsa Abedi Pele ya rattaba kwantiragi da Marseille a shekarar 1987, kuma yana cikin 'yan wasan da suka daukarwa kulob din kofin zakarun Turai a shekarar 1993.

Kanin Ayew Jordan shima ya buga tamaula a State Velodrome, kafin ya koma Lorient a watan Yulin bara.