Liverpool ta soke taro da Sterling

Raheem Sterling
Image caption Sterling shi ne ya lashe kyautar matashin dan kwallon da ya fi fice a Liverpool

Liverpool ta soke taron da ta shirya za ta yi da Raheem Sterling ranar Juma'a kan batun sabunta kwantiraginsa.

Liverpool ta soke taron ne bisa jawabin da eja dinsa Aidy Ward ya yi cewar dan kwallon ba zai rattaba sabuwar kwantiragi ba ko da an yi masa tayin £900,000 a duk mako.

Tun a baya Sterling ya ki amincewa da tayin da Liverpool ta yi masa na shirin bashi £100,000 a duk mako a baya, ana kuma hasashen zai nemi izinin barin kulob din a bana.

Liverpool ta ce ba ta ga dalilin da za ta tattaunawa da dan kwallon ba tun da eja din Sterling din ya ce dan kwallon ba zai rattataba kwantiragi ba koda nawa za a bashi.

Kwantiragin Sterling zai kare a Liverpool ne a karshen kakar wasan 2017, wanda ya taba sanar da Brendan Rodgers cewa yana son barin kulob din a ranar 10 ga watan Mayu.

An tsaida ranar Juma a domin nemo bakin zare tsakanin babban jami'in Liverpool Ian Ayre da Brendan Rodgers da Raheem Sterling kan batun zamansa a kulob din.