Toure zai koma Inter Milan - Zanetti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Toure ya haskaka sosai a City

Dan kwallon Manchester City da Ivory Coast Yaya Toure na gabda koma wa Inter Milan, in ji mataimakin shugaban kungiyar Javier Zanetti.

Toure mai shekaru 32, ana saran zai bar City a karshen kakar wasa ta bana, bayan ya kwashe shekaru biyar tare da kulob din.

Idan ya koma Inter, zai hade da Roberto Mancini wanda shi ne ya kai shi Man City.

Zanetti ya shaidawa mujallar Gazzetta dello Sport cewa "Muna wani mataki, kuma muna saran kamalla cinikin Yaya cikin kankanin lokaci."

Toure na daga cikin 'yan wasan da ke karbar £220,000 a duk mako, kuma a kakar wasa ta bana ya zura kwallaye 10 cikin wasanni 28 a gasar Premier.

A watan Afrilun 2013 ne Toure ya koma City daga Barcelona.