An fitar da Hull City daga gasar Premier

Steve Bruce Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bruce ya ce rashin mai zura kwallo a raga ne yasa suka yi ban kwana da Premier

Hull City ita ce kungiya ta uku da ta fice daga gasar Premier bana, bayan da ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Manchester United a KC Stadium.

Tun kafin su kara, Hull City ta sa ran za ta ci United sannan kuma West Ham ta doke Newcastle a wasan da suka yi ranar Lahadi

Amma sai hakan bai yi wu ba, a inda Newcastle ta casa West Ham da ci 2-0, kuma hakan ya ba ta damar ci gaba da zama a gasar Premier.

Haka kuma rashin cin kwallo a karawar da suka yi da Manchester United ya sa Hull City ta buga rabin wasanni 38 ba tare da ta ci kwallo ba.

Hull City ta kammala gasar bana a mataki na 17 da maki 35 daga cikin wasanni 38 da ta yi a bana, kuma hakan ya kawo karshen shekaru biyun da ta yi tana buga Premier.

Sauran kungiyoyin da suka fi ce daga gasar Premier bana sun hada da Burnley da kuma QPR.