Ina da rawar takawa a Liverpool — Rodgers

Brendan Rodgers Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rodgers ya yi shekaru uku bai dauki kofi a Liverpool ba

Koci Brendan Rodgers ya ce yana da gudunmawa mai yawa da zai bai wa Liverpool duk da doke su 6-1 da Stoke ta yi a gasar Premier ranar Lahadi.

Liverpool din ta buga wasan ne da nufin yi wa Steven Gerrard ban kwana, a shirin da yake yi na koma wa Aurka taka leda a badi.

Wannan dai shi ne karon farko da aka zazzagawa Liverpool kwallaye shida a wasa daya tun bayan shekaru 52 da suka wuce.

Liverpool din ta kammala gasar bana a mataki na shida a teburi da maki 62, sannan kuma ba ta dauki kofi ba a kakar wasannin bana ba.

Rodgers ya ce abu ne mai sauki idan mahukuntan kungiyar ba sa bukatar aiki na, sai su sallame ni, amma ina da gagarumar gudunmawar da zan bai wa Liverpool.

Kocin ya kara da cewar a bara da abubuwa suka ta fi yadda ya kamata ya sha yabo ta kowanne bangare, amma a bana an samu sauyi da ya saka shi cikin matsi.