Zan ci gaba da horar da Man City — Pellegrini

Manuel Pellegrini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man City ta kare a matsayi na biyu a gasar Premier da maki 79

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya ce yana da tabbacin cewar zai ci gaba da jan ragamar kungiyar a kakar wasan badi.

City ta kammala Premier shekarar nan a mataki na biyu, kuma ba ta dauki kofi ba a bana, yayin da ake ta yin jita-jita kan makomar kociyan a kungiyar.

Pellegrini ya shaida wa BBC cewar bai taba yin tantama cewar ba zai ci gaba da zama a City ba tun da aka fara kakar wasannin bana.

Ya kara da cewar ya yi magana da mahukuntan kungiyar, kuma ba mutane bane da za su sallame koci bisa dalilin rashin daukar kofi ba.

Sai dai kocin ya ce bai ji dadin yadda suka tunkari wasannin bana ba, domin sun yi sake an doke su a wasanni da dama, kuma hakan shi ne cikas din da suka samu.

Doke Southampton 2-0 da City ta yi a ranar Lahadi yasa ta ci wasanni shida a jere, tun daga lokacin da Manchester United ta doke ta 4-2.