Sam Allardyce zai bar West Ham United

Sam Allardyce Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kocin ya ce ya ji dadi da irin gudunmawar da ya bai wa kulob din

West Ham United ta sanar da cewar kociyanta Sam Allardyce zai bar kungiyar a karshen kakar bana, bayan da ya yi shekaru hudu yana jan ragamarta.

Allardyce, mai shekaru 60, shi ne ya kawo kungiyar gasar Premier daga Championship a shekarar 2012, sannan suka ci gaba da zama a gasar.

Kocin ya yi fama da kalubale daga wajen magoya bayan kungiyar a dukkan shekaru hudun da ya jogoranci West Ham.

A wani rahota da ta fitar, shugaban kungiyar David Sullivan da kuma David Gold sun yabawa Sam Allardyce da irin gudunmawar da ya bai wa kungiyar.

Haka kuma kungiyar ta ce ta fara shirye-shiryen nemo kociyan da zai maye gubinsa da kuma nemo kudin da za a kawo shi West Ham.

West Ham din ta kammala gasar Premier bana a mataki na 12, bayan da ta yi wasanni 38 ta kammala da maki 47.