Ba rashin jituwa tsakanina da Mikel — Keshi

John Mikel Obi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mikel ya dauki kofin nahiyar Afirka a Shekarar 2013 tare da Stephen Keshi

Kociyan tawagar kwallon kafar Nigeria Super Eagles Stephen Keshi ya karyata rade-radin cewar an samu rashin jituwa tsakaninsa da John Mikel Obi.

Keshi bai saka sunan Mikel ba a cikin 'yan wasan da za su kara da Chadi a wasan neman shiga Gasar cin Kofin Nahiyar Afirka a watan gobe.

Kocin ya ce bai zanta da Mikel ba a lokacin da yake yin jinya domin ya san girman rauninsa, dalilin da ya sa ke nan bai gayyace shi ba.

Rabon da Mikel ya bugawa Nigeria wasa tun a watan Nuwamba, amma Keshi ya ce kofa a bude take ga dan kwallon.

Haka kuma shi ma Elderson Echiejile wanda ke murza leda a Monacon Faransa, ba a gayyace shi ba zuwa tawagar Super Eagles din.

Keshi ya gayyato 'yan kwallon da suke murza leda a Turai su 15 wadanda za su hadu da wadanda suke wasa a gida a Abuja a makon gobe.