Real Madrid za ta nada Benitez

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rafa Benitez ya jagoranci Chelsea da Liverpool a shekarun baya

Ana saran za a nada Rafael Benitez a matsayin sabon kocin Real Madrid da zarar an kamalla gasar kwallon Italiya a ranar Lahadi.

Tsohon kocin Liverpool mai shekaru 55, a yanzu yana tare da Napoli kuma ya soma tattaunawa da Real a kan kulla yarjejeniya.

A ranar Litinin aka kori Carlo Ancelotti a matsayin kocin Real bayan shafe shekaru biyu a Bernabeu.

Ancelotti ne ya jagoranci Real ta lashe gasar kofin zakarun Turai a karo na 10.

Benitez ya lashe kofunan La Liga biyu da na Uefa tare da Valencia.

Kuma ya kasance tare da Napoli tun a shekara ta 2013 inda suka lashe kofin Coppa Italia a kakar wasan da ta wuce.