Bale zai ci gaba da wasa a Real Madrid

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gareth Bale ya yi fama da kalubale a Madrid a bana

Gareth Bale ya nuna alamun zai ci gaba da murza leda a Real Madrid duk da korar Carlo Ancelotti da kulob din ya yi.

Dan kwallon Wales, mai shekaru 25, ya rubuta a shafinsa na twitter cewar zai yi atisaye tukuru domin ganin ya koma kan ganiyarsa a Madrid a kaka mai zuwa.

An dade ana ta rade-radin cewar Bale zai sake komawa buga gasar Premier a badi.

Ana kuma sa ran Real Madrid za ta sanar da dauko kocin Napoli Rafeal Benitez domin ya jagoranci kungiyar.

Bale ya gamu da kalubale a shekara ta biyu a Madrid daga magoya bayan kulob din da kuma shan suka daga wajen 'yan jaridun Spaniya.

Madrid ta kare kakar wasannin bana ba tare da ta dauki kofi ba, yayin da Juventus ta fitar da ita daga kofin zakarun Turai a wasan daf da karshe.