Kungiyoyin Premier za su mamaye Turai

Chelsea FC Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce ta dauki kofin Premier kakar wasan bana

Kungiyoyin kwallon kafa dake buga gasar Premier za su mamaye wasannin Turai a shekaru hudu masu zuwa idan ba a cire dokar daidaita kashe kudin kungiyoyi ba.

Shugaban kungiyar Paris St-Germain Nasser Al-Khelaifi ne ya bayyana hakan a lokacin da aka yi hira da shi a wani shirin BBC.

Ya kuma ce wasannin Premier za su kara yin fice saboda yawan kudin shiga da gasar ke samu ta nuna wasanninta a talabijin ya karu zuwa £5.14bn.

Duk kungiyar da ta lashe kofin Premier badi za a bata £150m tukuicin daukar kofin, sannan a bai wa kungiyoyin da suka yi na karshe a gasar £99m.

A shekarar 2011 aka kirkiro dokar da ta hana kungiyoyi kashe kudade da dawainiyar da ta dara kudin da suke samu.

Sakamakon makudan kudaden da kungiyoyin Premier ke samu wajen tallata wasanninsu, sun fi sauran kungiyoyin Turai bin dokar.