West Ham za ta buga gasar Europa

West Ham
Image caption West Ham ta raba gari da kocinta Sam Allardyce

West Ham United ta samu gurbin shiga gasar Europa ta badi, sakamakon jan ragamar Premier a matsayin wacce ta fi buga wasanni bada gaba ba.

Hammers za ta kasance daya daga cikin kungiyoyi 104 da za su fara buga wasannin share fage da za a fara daga ranar 2 ga watan Yuli.

Shugabannin kungiyar David Sullivan da David Gold sun ce fara wasannin da za su yi a farkon Yuli zai sa su fuskanci kalubale mai yawa.

Daga kakar wasannin badi West Ham za ta bar filinta na Boleyn Ground domin komawa Olympic Stadium don ci gaba da wasanni daga 2016-17.

West Ham United wacce ta raba gari da kociyanta Sam Allardyce ta kammala Premier bana ne a mataki na 12 a kan teburi da maki 47.