Arsenal na tsoron haduwa da Benteke -Westwood

Christian Benteke Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Christian Benteke ya yi fama da jinyar rauni a farkon wasannin Premier bana

Dan kwallon Aston Villa Ashley Westwood ya ce 'yan wasan Arsenal na fargabar haduwa da za su yi da Christian Benteke a kofin kalubale a Wembley.

Westwood ya ce Christian Benteke, wanda ya ci kwallaye 12 a gasar Premier ya warke daga raunin da ya ji a baya, ya kuma dawo kan ganiyarsa.

Dan wasan ya kara da cewar Benteke kwararren dan kwallo ne wanda dukkan masu tsaron baya ke fargaba idan ya fuskance su.

Ashley Westwood ya koma Aston Villa taka leda a rana daya da Christian Benteke, wanda Paul Lambert ya dauko su ranar 31 ga watan Agustan 2012.

Arsenal za ta kara da Aston Villa a wasan karshe na cin kofin kalubale a ranar 30 ga watan Mayu a Wembley.